Nasiha

Sun Mayar da soyayya hanyar aikata badala, da sauran aiyukka na batsa!

Daga Abdullahi Muhammad Maiyama

Bazan iya kwatanta adadin ‘yan matanda akayi amfani da sunan soyayya aka gurbata rayuwar su ba, sau da yawa zaka tararda matashi yana soyayya da yarinya amma daga likacinda ya gurbata mata rayuwa bazai sake wai wayarta ba.

A yanzu haka akwai wani aiki na batsa da aka kawo a yanar gizo, dakuma kafafen sada zumunta na zamani irinsu facebook,WhatsaApp da dai sauransu.

Shidai wannan lamari ana kiransu SEX CHAT a turance, wato firar batsa kenan a hausance.
Itadai wannan mummunar hira tana gudana ne a wasu wurare da masoya maza da mada ke taruwa, domin hirarsu ta soyayya!
Sannan a wannan lokaci wasu matasa maza da mata sun mayarda wannan hira a matsayin wayewa! Wanda ta haka ake amfani wurin jefa wadanda basu shigaba a cikin wannan mummunar ‘dabi’a.
Duk yarinyarda bata yarda da wannan hira, dakuma yan rungume rungume zakaji ana cewa bata waye ba, ta zama bakauya, bagidajiya.

Sukuma samari duk wanda bashida budurwarda suke wannan lamari, shima ya zama bakauye!

Fitinar har ta fara gudana a wayoyi, dakuma kafafen sada zumunta, inda bayan anyi wannan hira a waya, sai kuma ayi yunkurin kusantar juna, domin yin yan rungume rungume, da shafe shafen juna, da tabe tabe.

Hatsari dakuma illoli na wauta da rashin kunya da suke dauremin kai gameda wannan fadala, zaka tararda yarinya tana daukar hoton jikinta ta aikawa wani baligi a whatsApp ko facebook, tare da batutuwa na iskanci da rashin kunya…

Tambayarda nikeda ita ga masu wannan aika, aika:-

Shin zaka iya aikata wannan abu a bainar jama’a ?

Shin zaka iya aikata wannan abu gaban iyayenka ?

Shin kanason a aikata irin wannan abu da mahaifiyarka, ‘yarka, dakuma kaunarka ?

Me yasa bakaso kuma ba zaka iya ba ?

Haba dan’uwa me yasa kake aikata fadala da iskanci gaban mahaliccin ka, sannan ba zaka iya aikatawa a gaban jama’a dakuma iyayenka ba ?
Haba dan’wa dan kasan tana sonka, ba zata iya juyama baya kake janta zuwa halaka ?

Shin ka manata da kannanka, ‘ya’yanka, dakuma mahaifiyarka ? ko kana tunanin zaka iya karesu daga irin wannan hallaka ?

Shin ko yaya kake ji idan ka tararda kaunarka, ko ‘yarka Tana Sex Chat da wani ?

Shin kanada masaniya gameda tsinuwar Allah akan wanda duk yaga tsiraicin wani ?

Haba kaunata, Anty ta, me yasa kike yarda ana gurbata miki rayuwa, kan soyayyarda batada amfani.
Da wadanme idanu zaki kalli mijinda ya aureki ?

Shi wanda ya gurbata miki rayuwa wanne kallo zai dinga yi miki da mijinki da ‘ya’yanki ?

Yakai dan’uwana, yake kaunata, yayata, mamata inaso kuyiwa kanku wadannan tambayoyi, sannan duk amsarda kuka samu kuyiwa kanku wa’azi dasu…

Rayuwa bata da tabbas!
Ka gaggauta tuba domin kada mutuwa ta riskeka kana aikata wannan danyen aiki.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.