Labarai

Sun lalata harsashin ginin barikin soji a Kaduna

Rikicin Kudancin kaduna ya janyo asarar rayuka da Sauransu
Wasu Sunje Sun Lalata Harsashin Da Aka sanya don Gina barkin soji A kudancin kaduna wanda wannan ne insha allahu ake ganin za,a dan samu zaman lafiya a wajan.

Gwamnatin tarayya ta yanke shawarar gina barikin soji Domin Kara tsaro A yanki.
A yan kwanakin bayane babban hafsan sojin yaje gurin domin daza harshin ginin barikin sojin.

To sai dai wasu bata-gari sun lalata wannan harsashe da aka aza.Wannan lamari dai ya sa wasu ‘yan kudancin jihar suka yi Allawadai game da lalata harsashin ginin Barikin Soji da aka girka. 

An aza harsashin ne makwanni biyu da suka gabata domin gina barikin soji a Kafancan don kai daukin gaggawa idan wani rikici ya barke ko aka kai wani hari a Kudancin jahar.
A ganin wasu dai lalata wannan harsashin gini na barikin soji wata alama ce dake nuna adawa ga matakan da gwamnati ke dauka na samar da zaman lafiya a Kudancin na jahar Kaduna.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement