SUBHANALLAH: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Sha Uku A Jihar Neja

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kimanin mutane goma sha uku ne ƴan bindiga suka hallaka a garin Mangwaro dake ƙaramar hukumar Mariga. Yayin da aka kawo mutane ashirin da 22 a asibitin Kontagora. Waɗanda ƴan bindigar suka harba tare da raunatawa, wanda daga bisa ni ɗaya daga cikin su yace ga garin ku. Jimillan mutane 14 kenan da suka rasu a harin na yau.

Saidai al’ummar garin sun tabbatar da sun fatattaki ƴan bindigar tare da hallaka dadaman su, duk su na gudu da gawarwakin ƴan uwan na su.

Muna ƙara kira ga gwamnati da ta dubi halin da wannan yanki na mu ke ci ki. Domin da sannu sannu ana cigaba da cin mu da yaƙi🙆‍♂️

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 773

Ya Allah ka agazawa yankin mu

Daga Comrade-Zakari Y Adamu Kontagora

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: