-Advertisement-


Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Su Waye Zasu Maye Gurbin Jaruman Fim Din Mujadala?


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shirye-shirye sun yi nisa domin sake shirya fim din Mujadala, wanda aka fara yi shekara 18 da ta gabata, kamar yadda kamfanin da ke shirya fim din ya bayyana.

Kamfanin Mai Shadda Investment ya ce za a fara nadar shirin a ranar 10 ga watan Mayu.

Jarumi Umar M Shareef shi ne zai maye gurbin marigayi Ahmad S. Nuhu, wanda shi ne ya fito a matsayin jarumi a fim din na asali.

Fim din Mujadala ya shahara sosai a tsakanin ma’abota fina-finan Hausa.

Fitaccen jarumi kuma mai shirya fim Ali Nuhu, wanda dan uwa ne ga Ahmad S. Nuhu, shi ne zai tsara fim din da kuma bada umarni.

Marigayi Ahmad S. Nuhu ya mutu ne a farkon shekara ta 2007 bayan wani mummunan hadarin mota da ya yi a hanyar Azare zuwa Maiduguri.

Mutuwarsa ta tayar da hankalin masu ruwa da tsaki a Kannywood da kuma magoya baya.

Ya kasance jarumi mai tashe da farin jini, wanda kuma aka ce abokan aikinsa na jin dadin hulda da shi.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 331

- Advertisement -

Kamfanin Mai Shadda ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa Mujadala shiri ne wanda har yanzu ‘yan kallo “suna daukin gani bayan shekara kusan 18 da fitowarsa”.

GA SUNAYEN JARUMAN DA ZASU MAYE GURBIN.

Umar M Shareef – Ahmad S Nuhu

Abdul M Shareef – Ali Nuhu

Maryam Yahya – Abida Muhammad

Bilkisu Shema – Fati Muhammed

Hasana Muhammad – Maijidda Abdulkadir

https://www.youtube.com/watch?v=S1OV5BOr-Gs

DOWNLOAD VIDEO HERE 

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.