dama mutumin yana cikin wadanda sojoji ke nema ruwa a jallo tun 2012
DAGA HAUSA TIMES: Hukumar yansandan farin kaya (SSS), a ranar Asabar sun sanar da samun nasarar kama, Husseini Maitangaran, wani kasurgumin kwamandan Boko Haram da ya shahara wajen hada Bama-Bamai da kai manyan hare-hare.
Sanarwar da kakakin rundunar, Tony Opuiyo ya fitar yace tun a 2012 ake neman mutumin ruwa a jallo.
Sanarwar tace Maitangaran ya jagoranci kai hare-hare da dama da suka hadar da harin da aka kai a ofishin mataimakin sufeta janar na yan sanda (AIG zone 1) a ranar 20 ga watan Janairu 2012, da wasu wurare-daban daban a Kano.
Sannan shine ya jagoranci kai hari a babban masallacin juma’a na jihar Kano da wata cibiyar bayanai ta sojoji dake Yobe, inda mutane sama da 100 suka mutu a 2015.
Hausa times ta ruwaito daga majiya mai tushe cewa bayan kama Maitangaran din, ya taimakawa hukumar SSS din da bayanan da suka taimaka aka kama wasu ragowar kwamandojin na Boko Haram da suka hadar da, Abdulkadir Umar Mohammed, a kasuwar Kantin Kwari dake karamar hukumar Fagge, Sai wani Muhammad Ali da aka kama a Sheka dake karamar hukumar Kumbotso duk a jihar Kano.
Sanarwar SSS din tace duka mutanen Biyu sun shigo hannu ne sa’ilin da suke shirya yadda zasu kai hare-hare a Abuja, Kano, Kaduna, Bauchi, Yobe, Naija da Borno a lokutan sallar layya (Babbar sallar idi) da akayi daga 1 zuwa 4 ga watan satumbar nan wanda basu samu nasarar aiwatarwa ba sakamakon kama su da akayi.
Hausa times ta kuma ruwaito rundunar SSS din ta kama wasu jagororin Boko Haram din, Yahaya Mohammed Abatcha da Yusuf Mohammed a Tunga cikin Minna jihar Naija wadanda aka bawa damar shirya hare-haren Kaduna, Naija da Abuja a lokutan bukukuwan sallar.
Kazalika an kama wani dan kato da gora, Abdulkarim Mohammed wanda akafi sani da Baba Maigiwa.
An kamashi ne a Ajilani dake karamar hukumar Jere a jihar Borno.
Baba Maigiwa, ya fake da taimakawa jami’an tsaro ashe kasurgumin dan leken asirin Boko Haram ne wanda shi ke baiwa mayakan bayanai game sa sojoji a Maiduguri.
SSS sun kama kwamandan Boko Haram da ya jagoranci kai hari babban masallacin juma'a na jihar Kano

Add Comment