Labarai

An Soke Ra'kumi A Gangamin Murnar Dawowan Shugaba Buhari

Daga Ahmadu Manaja Bauchi
Bayan gudanar da gangamin, murnan dawon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, jiya Asabar a garin Bauchi yau lahadi matasa magoya bayan Shugaba Buhari, karkashin jagorancin Shugaban matasan jam’iyan APC, na jihar Bauchi Alh Nasiru A Kasa A Tsare.
 
Shugaban Matasan jamiyan APC, ya shaidawa wa jaridar RARIYA cewa ya soke wannan rakumi ne, domin godiya ga Allah da ya bawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari lafiya, har ga shi ya dawo.
Shugaban matasan ya yi fatan Allah ya kara wa Shugaban kasa lafiya domin ya cigaba da mulkin najeeiya Shugaban matasan yace mulkin Buhari, rahama ga mu mutanen Arewa maso gabas da a ci gaba da mara wa Shugaban kasa da gwamnatin sa baya domun suyi nasara
Shugaban matasan ya nuna jin dadin sa da ya ga Shugaba Buhari ya dawo
lafiya har ya dawo lafiya
Bayan wannan gangami na Shugaban matasa a gobe Litinin ma akwai wani Gagaruman gangami na Magoya bayan Shugaba Buhari a garin Bauchi.
A karshe an gudanar da addu’o’in samun lafiya ga Shugaban kasa Muhammadu da fatan Allah ya kasa masa lafiya ya Shekara Takwas na mulkin najeriya amin.