Labarai

Sojojin sun shiga wani kauye a jihar Edo,sun tashi mazauna kauyen sabo da rikicin filaye

-Yan kauyan sun koma fadar sarki da zama

– Mutane sun zama yan gudun hijra a garin su

– Gwamna Obaseki ba taba cin hakkin mutanen sa ba

 

Daruruwan iyalai wanda suka hada da yayan su, sun rasa gidajen su a garin Oghede dake karamar hukumar Ovia na jihar Edo a dalilin su nace wa, filayensu mallakar sojoji ne.

Yan kauyen sun koma da zama a fadar sarkin Oghede, mai martaba Osadebamein Aghaghowa, yan kauyen sun zama yan gudun hijira a garin su. Sojoji sun mamaye kauyen ne a safiyan Alhamis, suka fatataki mutanen daga gidajen su, suka nakasa wa’yanda suka yi taurin kai

 

Tashin hankali a cikin al’umma ya tilasta Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya tura shugaban ma’aikata na jihar, Mr. Taiwo Akerele zuwa yankin,a ranar Asabar, don kauce wa zub da jini.

 

Enogie Aghaghowa, a makon da yagabata ya jagoranci yan kauyen yin zanga-zanga zuwa gidan, Oba of Benin Oba Ewuare 11 dan nuna rashin amincewan su da kwace musu filaye da sojoji suka yi.

Sojojin sun shiga wani kauye a jihar Edo,sun tashi mazauna kauyen sabo da rikicin filaye

Duk da haka, shugaban ma’aikata jihar Edo, mista Akerele, ya ziyarci wajen, ya kuma yi watsi da zargin da ake wa gwamnan jihar game da ce wa shi ya turo sojoji su kwace musu filayen su. Ya tabbatar da cewa Obaseki ba zai taba hada kai da wasu ba dan cin hakkin mutanen sa.

Sojoji suna ikrarin cewa yan kauyen sun shigo musu cikin filayen su, amma yan kauyen sun musunta haka sun ce filayen sojojin bai karaso wajen da suke zama ba

Sojojin sun ce za su kira taro dan tattauna yadda za a kawo karshen rikicin, kuma za a gayyaci shugaban masu auna filaye na jihar.

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement