-Advertisement-


Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Sojojin Najeriya ‘sun kashe’ ‘yan Boko Haram 16 a Borno


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Dakarun rundunar Operation Fire Ball ta sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP guda 16 a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

Muƙaddashin shugaban sashen yaɗa labaran rundunar, Bernard Onyeuko ne ya bayyana haka ranar Lahadi cikin wata sanarwa, yana mai cewa Operation Fire Ball wani ɓangare ne na rundunar Operation Lafiya Dole da ke yaƙi da ‘yan ta’adda.

Birgediya Janar Onyeuko ya ce dakarunsu sun lalata motar bindiga guda huɗu na ‘yan ƙungiyar tare da ƙwato akwatun harsasai yayin harin.

Ya ce a ranar 21 ga Oktoba sun kula da wasu motoci suna bin bayan jerin gwanon motocinsu da ke kan hanyar mayar da ‘yan gudun hijira garin Baga daga Maiduguri, suna ƙoƙarin shiga cikinsu.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 646

- Advertisement -

A cewarsa, dakarun sun far musu nan take, inda suka kashe uku daga cikinsu tare da lalata motar bindiga ɗaya.

Kazalika, dakarun da ke sansanin Army Super Camp a Magumeri sun kashe mutum 11 a wata arangama da suka yi sannan suka kama wasu makaman harbo jirgi guda uku, a cewar Mista Onyeuko.

Bayan wannan fafatawar ne kuma aka kashe wasu guda biyu yayin da wasu suka tsere da munanan raunuka.

A jiya Asabar ma sai da jami’an tsaro suka kashe ‘yan Boko Haram shida a Jihar Yobe mai maƙwabtaka, yayin wani hari da ‘yan Boko Haram suka kai a garin Babban Gida. Ɗan sanda ɗaya ya rasa ransa a fafatawar.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.