Labarai

Sojoji sun zagaye ginin majalisar dinkin duniya a Maiduguri bisa zargin makamai

Sojoji sun zagaye ginin majalisar dinkin duniya a Maiduguri bisa zargin makamai

…ana kuma zargin Shekau na cikin gidan

Rahotanni daga jihar Borno suna bayyana cewa sojoji sun zagaye ginin majalisar dinkin duniya dake Maiduguri bisa zargin an shiga da makamai cikin akwatuna a gidan.

Majiya mai tushe ta wallafa cewa tun da misalin karfe 2:00 na dare sojojin sukayiwa gidan kawanya inda suka nemi shiga cikin gidan domin binciken makamai da rundunar farin kaya ta SSS ta tsegumta masu cewa an shigar dasu a cikin gidan.

Hausa times ta ruwaito daga majiyar cewa anyi-ta kai ruwa rana tsakanin masu tsaron gidan da bataliyar sojoji wanda sai kusan karfe 7:00 na safiyar yau Juma’a sojojin suka samu ikon kutsawa gidan a inda suka bincika ko’ina basu ga komi ba a cewar rahoton

Gidan wanda akeyiwa lakani da Red Roof gidane da kungiyoyin agaji na majalisar dinkin duniya ke zama a ciki na wucin gadi.

Bayanai sunce faruwar wannan lamari ya fusata kungiyoyin sa-kan a inda aka fasa kawo kayan tallafi da wasu jirage ke shirin kawowa jihar ta Borno daga majalisar Dinkin Duniya.

Hausa times ta kuma ruwaito majiyar na cewa kayayyakin gini ne a cikin akwatunan da aka shigar cikin gidan wanda hukumar SSS din ta tsegumtawa sojoji bisa zargin makamai ne.

Bayanai sunce sojojin sun janye daga ginin bayan da suka bincikeshi basu ga komi ba.

Kawo yanzu dai duka bangarorin biyu sunyi alwashin fitar da sanarwa akan hakikanin abunda ya faru.

Zagaye gidan dai yana zuwa ne kwanaki guda da aka yita yada jita-jita a kafafen sadarwa cewa ana zargin a gidan ne shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya boye.

Ya kuke kallon wannan lamari?

 

@Hausa Times