Sojoji Sun Damke Mayakan Kungiyar Boko Haram Goma A Jihar Kano, A Yayin Da Suke Kokarin Kai Hari Masallaci

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Comr Abba Sani Pantami
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin sun kama mutanen lokacin da suka kutsa Filin Lazio dake yankin Hotoro a cikin garin Kano da yammacin ranar Asabar.

Wadanda aka kama din sun yi kokarin kai hari ne a wani masallaci da kuma wasu gidaje dake yankin, sai dai rahotanni sun nuna cewa farmakin yazo dai-dai lokacin da musulmai ke shan ruwa bayan sun kai azumi.

Wannan lamarin dai ya sanya tsoro sosai a zukatan mazauna yankin.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 773

An gano cewa masallacin da suka yi kokarin kai harin mallakin wasu mutane yan asalin jihar Borno ne, wadanda suka baro gidajensu saboda rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a arewa maso gabas.

Haka nan kuma, An gano cewa jami’an sojin, sun tattara wasu abubuwa da ba’a gane su ba a kewayen masallacin.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar sojoji, Mohammed Yerima, yayi alkawarin yiwa manema labarai bayani ranar Lahadi.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: