Sojoji Sun Chafke Me Yiwa Yan Boko Haram Safarar Makamai


0 423

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa jami’an soji na Atisayen lafiya dole sun kama wasu makamai na ƙasar waje tare da mai shigo da makaman ga ƴan ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram da kuma ISWAP wadda ta ɓalle daga jikin Boko Haram.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 627

-Advertisement-

Bayanan sun fito daga bakin mai gudanar da sashen labarai na na hukumar tsaro,Manjo janar.John Enenche,lokacin da yake ƙarin haske game da irin nasarar da atisayen sojoji ke samu a ranar Alhamis a garin Abuja.

Eneche ya ce mai laifin wanda ya kasance ɗan ƙasar Najeriya,an kama shi a kusa da sansanin ƴan gudun hijira a yankin Diffa dake Jamhuriyar Nijar a ranar 3 ga watan oktoba.

Enenche yace hukumar soji ta yabawa sojojin a bisa wannan bajimtar.

Kuma suna ƙarfafawa mutane guiwa da su cigaba da bada bayanai da zasu taimaka musu wajen cimma nasara.

Ya ƙara da cewa sun yi nasarar kama mai laifin biyo bayan tattara bayanan sirri akan ƴan ta’adda a ƙauyen Chinguwa dake ƙasar Nijar kusa da Gashigar a ƙaramar hukumar Mobbar dake Jihar Borno.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.