Labarai

Sojoji Sun Ceto Sojan Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A NDA

Daga Sulaiman Ibrahim,
Manjo kanal Datong, wanda aka yi garkuwa da shi lokacin da ‘yan bindiga suka kutsa cikin Kwalejin Tsaron Nijeriya (NDA) a Kaduna, a watan da ya gabata, ya kubuta.

An kashe manyan jami’ai biyu a lokacin da lamarin ya faru a ranar 24 ga Agusta, 2021.

A daren Juma’a, Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Runduna ta 1, Sojojin Nijeriya, Kanal Ezindu Idimah, ya ce sojoji sun ceto Datong.

Ya ce shirin da ya kai ga kubutar da sojan ya janyo tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda da aka gano a yankunan Afaka da Birnin Gwari na jihar.

Ya ce an kashe dimbin ‘yan bindiga a yayin farmakin, musamman, a ranar 17 ga Satumba, 2021.

Ya yaba da kokarin rundunar sojin sama ta Nijeriya (NAF), DSS, ‘Yan sandan Nijeriya da ‘yan Nijeriya masu kishin kasa saboda tallafin da suka bada wanda yakai ga nasarar ceto manjon.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: