Dakarun dake karkashin rundunar “Operation Lafiya Dole” sun samu nasarar cafke wasu mata biyu da suke dauke da bama-bamai a jikinsu, dakarun sun samu wannan nasarar ne jiya da maraice a karamar Konduga ta jihar Bornu. Rundunar sojin Nijeriya ce ta bayyana wannan nasarar da rundunar ta samu a shafin sada zumuntan ta na Twitter, rundunar ta bayyana cewa ‘yan kunar bakin waken biyu sun yi kokarin shiga wani sansanin soji ne a daren jiya Laraba don tayar da bama-baman.
Dakarun rundunar sun samu nasarar kwance bam din da ke daure a jikin matan biyu, sannan sun ce suna kan gudanar da bincike don gano gaskiyar lamari akan ‘yan kunar bakin waken. Dakarun sun samu nasarar cafke ‘yan kunar bakin waken ne da misalin karfe 9:30 na dare a daidai wani kauye Mushimari da ke karamar hukumar Konduga na jihar Bornu, inda suke kokarin kutsa kai cikin sansanin bataliya ta 222 dake aikin samar da zaman lafiya a yankin