Labarai

Sojoji Ne Ba Sa So Yaki Da Ta’addanci Ya Kare, Cewar Sheikh Gumi

Daga Suleiman Abba (TBABA)

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi zargin cewa sojojin Nijeriya na amfana da yaki da kasar ke yi da ta’addanci shi ya sa ba sa so matsalar ta kare.

Malamin ya yi zargin cewa zunzurutun kudaden da ake kashewa wurin yaki da ta’addanci ya sa yawancin manyan sojoji ba sa kaunar a kawo karshen matsalar.

“Sojoji ba sa taimakawa ko kadan saboda su ke cin amfana da tabarbarewar sha’anin tsaro,” inji shi a lokacin hirar da gidan talabijin na ARISE TV ya yi da shi.

Sheikh Gumi ya bayyana haka ne yayin karin haske game da ziyarar kwanan nan da yake kaiwa dazuka don yin da’awa ga ’yan bindiga su rungumi zaman lafiya su daina ta’addanci.

“A shirye ’yan bindigar suke su ajiye makamansu su koma rayuwarsu yadda suka saba a baya muddin Gwamnatin Tarayya za ta biya bukatarsu da bata taka kara ta karya ba: ta gina musu makarantu da sibitoci ta samar musu da ruwan sha.

“Suna yawan kokawa cewa sojoji na kashe mutanen da babu ruwansu. Shi ya sa suka fara daukar makamai. Ko ta ina suke samun makamai? Suka fara yin garkuwa mutane wanda shi ya haifar da wannan aikin soji.

“Amma a shirye suke su ajiye makamansu su koma rayuwa kamar sauran ’yan Najeriya idan za a gina musu makarantu da asibitoci a samar musu da ruwan sha.

“Akwai kuma zargin cewa sojoji ba sa so a kawo karshen rikicin saboda da biliyoyin Nairori da ake ba su don yakar ta’addanci. Saboda haka su ma sojojin ba sa taimakawa.

“Ina yaba wa ’yan sanda da Shugaban ’Yan Sanda musamman saboda ya taimaka mun je mun gana da waddannan mutane; amma su sojoji babu alamar za su taimaka, ba su ba da hadin kai ba; ban san dalili ba.”

#Rariya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: