Labarai

Sojin Nijeriya Sun Yi Zanga-zanga Kan Rashin Isassun Makamai

Daga Tukur Sani Kwasara
Rundunar Operation Lafiya Dole sun gudanar da zanga-zanga kan tura su faggen yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram, kamar yadda Jaridar legit ta ruwaito.

A cewar majiyoyi daga barikin Maimalari, Sojojin sun mamaye hedkwatar Operation Lafiya Dole ne a daren Alhamis suna harba bindiga sama.

Sun bayyana cewa suna zanga-zanga ne sakamakon rashin biyansu alawus da kuma rashin isassun makaman yaki.

A jawabin wasu daga cikin sojojin da suka bukaci a sakaye sunayensu, sun bayyana yadda yan ta’addan Boko Haram suka hallaka Sojoji a harin Marte saboda makaman yan ta’addan sun fi nasu.

Channels TV ta bayyana cewa kakakin rundunar Operation Lafiya Dole, Kanal Isa Ado, ya tabbatar da labarin.

Wannan zanga-zanga na Soji ya biyo bayan fallasan da NSA Babagana Munguno yayi cewa an nemi kudin makamai an rasa karkashin tsaffin hafsoshin tsaro.

Mai baiwa kasa shawara kan lamarin tsaro, Babagana Monguno, ya yi zargin cewa wasu kudaden da aka baiwa tsaffin hafsoshin tsaro domin sayan makamai sun yi batan dabo.

A cewar Monguno, an bada kudaden ne domin sayen makamai don karfafa yakin yan ta’addan Boko Haram.

NSA Monguno ya yi wannan fallasa ne a hirar da yayi da BBC Hausa ranar Juma’a, 12 ga Maris.

Amma mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa ba zai yiwu a ci kudin makamai karkashin shugaba Muhammadu Buhari ba.

Shehu ya bayyana hakan a shirin Politics Today na ChannelsTV ranar Juma’a inda yace kudi $1billion da aka saki a 2018 don sayen makamai, an yi amfani da su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: