Wasanni

Smith Rowe Zai Zama Babban Dan Wasa A Arsenal – Henry

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Thierry Henry, ya bayyana ra’ayinsa akan matashin dan wasan kungiyar, Smith Rowe, wanda ya sake sabuwar yarjejenjiya da kungiyar a satin daya gabata.

A ranar Alhamis ne Emile Smith Rowe ya saka hannu kan doguwar yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal kamar yadda kungiyar ta bayyana a shafinta na yana gizo tare das aka hoton matashin dan wasan.

Dan wasan mai shekara 20 a duniya, wanda ya fara buga wasa a Arsenal tun daga matasan kungiyar, kungiyar kwallon kafa ta Aston Billa ta taya shi har karo biyu, amma ba a sallama mata shi ba.

“Duk wanda yake bibiyar yadda Smith Rowe yake buga wasa tabbas zai fahimci cewa nan gaba kadan zai zama babban dan kwallo a duniya wanda hakan ba zai samu ba sai idan ya samu horo mai kyau da kuma wasanni da dama” in ji Henry

Smith Rowe ya fara yi wa Arsenal wasanni a Premier League a kakar wasa ta shekarar 2020 zuwa 2021, wanda ya ci kwallo biyu ya kuma bayar da guda hudu aka zura a raga a kakar da ta wuce.

Kuma an bai wa Smith Rowe riga mai lamba 10 da zai saka a kakar wasa ta shekarar 2021 zuwa 2022, wadda tsofaffin ‘yan wasa irinsu Dennis Bergkamp da kuma Mesut Ozil suka yi amfani da ita a kungiyar a shekarun baya baya.

Aston Billa ta taya shi fam milian 25 da fam miliyan 30 ga dan kwallon tawagar Ingila ta matasa ‘yan kasa da shekara 21,wanda saura kwantiragin kakar wasa biyu ya rage kafin yanzu da ya kara kulla wata mai tsawo.

Kociyan kungiyar ta Arsenal, Mikel Arteta ya bayyana cewa bashi da niyyar sayar da dan kwallon wanda ya taka rawar gani a wasannin aro da ya yi a kungiyar RB Leipzig da kuma Huddersfield Town.

Tuni kungiyar ta Arsenal ta sayi dan wasa Lokonga daga kungiyar kwallon kafa ta Anderletch ta kasar Belgium sannan kuma ta cimma yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Brighton Hobe Albion domin daukar dan wasan baya na kungiyar, Ben Whites, dan asalin kasar Ingila.

A cewar kociyan kungiyar, Arsenal za tayi kokarin sayan sababbin ‘yan wasa domin ganin ta tunkari kakar wasa mai zuwa da kafar dama kuma tuni kungiyar take fatan sayan karin wasu ‘yan wasan musamman na tsakiya domin ganin ta sake komawa buga kofin zakarun turai na Champions League a kakar wasa mai zuwa bayan da kungiyar ta shafe kusan shekara biyar ba tare da buga gasar ba saboda rashin samun tikiti.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.