Siyasa

Siyasa: Muna goyon bayan sake fasalin kudin tsarin Najeriya dari bisa dari – Inji hadin gwiwar jam’yyun 15

 

– Wani kungiyar hadin gwiwar jam’iyyun

– Wani kungiyar hadin gwiwar jam’iyyun siyasa ta ce ta na goyon bayan sake fasalin kudin tsarin Najeriya

– Shugaban hadin gwiwar ta kasa ya ce burin su shine ta yadda za a samar da wata sabuwar Najeriya

– Hadin gwiwar ta kunshi jam’iyyun siyasa 15

siyasa ta ce ta na goyon bayan sake fasalin kudin tsarin Najeriya

– Shugaban hadin gwiwar ta kasa ya ce burin su shine ta yadda za a samar da wata sabuwar Najeriya

– Hadin gwiwar ta kunshi jam’iyyun siyasa 15

Akalla jam’iyyun siyasa 15 a karkashin hadin gwiwa sabuwar Najeriya wato “Coalition for New Nigeria” (CNN)sun nuna goyon baya ga sake fasalin kudin tsarin kasar.

Shugaban CNN ta kasa, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam wanda ya bayyana wa manema labarai a ranar Litinin, 24 ga watan Yuli a Abuja cewa hadin gwiwar na goyon bayan sake fasalin kudin tsarin Najeriya dari bisa dari don samar da wata sabuwar Najeriya.

Abdulsalam ya ce burin hadin gwiwar shine ta yadda za a zamar da amintacciya da wadata ta hanyar tasiri shugabanci a kasar.

Majiyar Arewablog.com ta tabbatar da cewar, hadin gwiwar na da jam’iyyun siyasa 15 wanda ta hada Labour Party, African Democratic Congress, National Action Council, Democratic People’s Congress, Progressive People’s Alliance, People for Democratic Change da Democratic Alternative.

Sauran sun hada da Better Nigeria Progressive Party, Action Alliance, United Democratic Party, Peoples Party of Nigeria, Advanced Congress of Democrats, Young Democratic Party da kuma Mega Progressive Peoples Party.

 

Source Naij.com