– Kungiyoyin matasan Najeriya sun bukaci gwamna Dankwambo ya fito neman shugaban kasa a shekarar 2019
– Kungiyoyin matasan tace za ta marawa Dankwambo baya dari bisa dari
– Matasan sun ce kasancewar gwamnan Gombe yasa suke bukatar ya fito zaben 2019
Wasu kingiyoyin matasan Najeriya sun bukaci gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo da ya shiga gazar neman shugaban kasa a zaben shekarar 2019.
Gwamnan wanda shi kawai ya samu zarcewa a wa’adin na biyu a zaben 2015 a matsayin gwamna a duk yankin arewa a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP.
Hadin gwiwar kungiyoyin matasan Najeriya a lokacin da suka tashi daga wani taron kwanaki biyu a birnin Abuja, sun bukaci gwamna Dankwambo da ya saya takara shugaban kasa a shekarar 2019. Kungiyoyin matasan sun yi alkawarin mara masa baya dari bisa dari.
Arewablog.com ta tattaro cewa bangaren zartarwar kungiyar na kasa wato Democratic Youths Alliance, (Dya), a karshen makon nan ta nuna goyan baya ga Dankwambo.
A cewar wata sanarwa dauke da sanya hannun Tersoo Yisa da kuma Daniel Fajana, a madadin kungiyar, cewa sun yanke shawarar mara ma Dankwambo baya ne a lokacin da suke nema matasa wanda ya cicinta kuma daga yankin arewa don ya fito shiga takara a zaben 2019. Wannan mataki ya dogara ne a kan shekarunsa a matsayin matashi da kuma ayyukansa na inganta rayuwa a matsayin gwamnan jihar Gombe.
Add Comment