Wasanni

Sir Alex Ya Soki Solkjaer Saboda Ajiye Ronaldo A Benci

Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Sir Alex Ferguson ya ce ya kamata a ce Manchester United ta fara da Cristiano Ronaldo a gasar Premier League da ta kara da Everton a karshen satin da ya gabata. Ranar Asabar din da ta gabata ce Manchester United ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Everton a wasan mako na bakwai a babbar gasar Ingila da suka tashi wasa 1-1 a filin wasa na Old Trafford.

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar, Ole Gunnar Solskjaer bai fara wasan da Ronaldo da kuma Paul Pogba ba da suka yi zaman benci, sai da aka koma zagaye na biyu ya saka su a fafatawar. Ronaldo ya shiga karawar lokacin da United ke cin kwallo daya, inda daga baya
Everton ta farke da ta kai suka tashi 1-1 a wasan, sannan kawo yanzu Ronaldo ya ci kwallo biyar a wasa takwas da ya buga wa Manchester United, wanda ya koma a bana daga Jubentus.

Kyaftin din tawagar Portugal ya bayyana cewar Sir Ferguson ya taka rawar gani da ya amince ya sake komawa Old Trafford a karo na biyu a lokacin da ya yi wata hira da manema labarai a Ingila. Manchester United ta hada maki 14 a wasa bakwai a Premier League, za kuma ta fafata a wasan gaba da Leicester City ranar 16 ga watan Oktoba, kuma a wasan dan wasa Marcus Rashford zai dawo daga doguwar jinya

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement