Kannywood

Silar Batanci Ga Annabi Muhammadu: Na Cire Rahama Sadau A Fim Dina

Fitaccen mai shirya Finafinan Hausa, kuma mataimakin hadaddiyar Kungiyar ‘yan Hausa Fim ta kasa wato MOPPAN, Sani Sule Katsina, ya bayyanawa `Kannywood Exclusive` cewa ya cire Rahama Sadau a sabon fim din sa mai suna MAKAHON DAJI wanda zai fara dauka a ranar 20, ga wannan watan na Nuwamba.

Sani Sule Katsina, ya ce ba zai sanya wadda ta yi sanadin aka yi batanci ga Manzon Allah (S.A.W) a fim din sa ba, domin babu abin da ya fi so a duniya da lahira kamar Annabi Muhammadu (S.A.W).

Kafin wannan badakalar Rahama Sadau tana cikin jerin jarumai mata da za su taka rawa a sabon shirin fim din wanda ya tattara manyan Jaruman Kannywood cikin sa.

Sauran jaruman da za su fito a cikin shirin sun hada da Adam A. Zango, Sadik Sani Sadik, Falalu A. Dorayi, Tijjani Asase, Maryam Yahya, Zaharaddini Sani, Isah A. Isah, Amal Umar da sauran su.

Ana sa rana ranar Litinin za a bayyana wadda za ta maye gurbin Rahama Sadau a wannan katafaren shirin fim da za a fara daukar sa.

A ganin ku wace jaruma ya kamata ta ye maye gurbin ta?

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.