Labarai

Shugabanni majalisar tarayya sun so zuwa ganin Buhari amma aka hana su

Wata majiya mai tushe da bata so a bayyana sunan ta a kafafen yada labarai ta bayyana wa majiyar mu ta Punch yau Lahadi cewar shugabannin majalisar tarayya sun so suje ganin Buhari a Landan amma aka hana su.

Haka ma dai majiyar ta cigaba da cewa yanzu haka dai shugabannin majalisar ta tarayya Yakubu Dogara da kuma Bukola Saraki suna cikin shirin ko ta kwana da kuma jiran a basu dama don su je gano shugaban.

Arewablog

ta tsinkayi majiyar tamu yana cewa: “Da yake fadar shugaban kasa ce kadai ke da ikon zabar wanda suke so yaga shugaban, yanzu haka dai ba’a gayyaci shugabannin majalisar ba.”

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya dai wasu jigajigan jam’iyyar APC din da kuma gwamnonin wasu jihohi sun yi tattaki har Landan din domin ganawa da shi.

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.