Labarai

Shugaban Wata Jami’a A Arewa Ya Yiwa Daliban Da Suka Samu Carryover Afuwa

Shugaban Jami’ar Yar’aduwa University Katsina Yayi Wa Ɗaliban Da Suka Samu Carryover Afuwa

Daga Kamalancy

A wani labarin da muke samu yanzu mai dadin ji ga daliban Jami’ar Umaru Musa Yar’aduwa dake Katsina, shugaban Jami’ar Farfesa Sanusi Mamman Malumfashi ya yi afuwa ga wasu daliban Jami’ar da suka gaza amsar sakamakonsu sakamakon yawan carryover da suka samu.

Kamar yadda Aminu Aliyu Tanko ya rawaito mana, ya bayyana cewa;

“Shugaban Jami’ar Umaru Musa Yaradua university dake Katsina Professor Sanusi Mamman Malumfashi ya yi afuwa ga duk wadanda suka gama cinye shekarunsu na degree amma ba su gama ba, da su dawo domin su karasa su amshi sakamakonsu.

Farfesa ya kafa sharudda kamar haka;

1- Dole ne ya zama ba satar amsa suka yi ba aka koresu.

2- Sannan kuma kwasa-kwasan da za su gyara basu wuce goma ba.

3- Duk wanda makinsa CGPA ya gazama 1.50 amma ya kai 1.00 shima ya zo.

Allah yakara azurtamu da jagorori irin Farfesa Sanusi Mamman Malumfashi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: