-Advertisement-


Shugaban Majalisar Dattawa Saraki Ya Amsa Tambayoyi A Gaban `Yan Sanda


0 78

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shugaban Majalisar Dattawa Saraki ya amsa tambayoyi a gaban ‘Yan Sanda

-Advertisement-

-Advertisement-

Mun samu labari cewa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ya mika kan sa gaban Rundunar ‘Yan Sandan Kasar game da bincikensa da ake yi kan wani fashi da aka yi a Jihar Kwara.

Bukola Saraki ya je gaban ofishin ‘YanSanda jiya

A jiya ne dai tsohon Gwamnan Kwara kuma Sanata a yanzu Bukola Saraki ya tashi ta-ka-nas har gaban Jami’an ‘Yan Sandan Kasar domin amsa gayyatar da aka yi masa na zargin taimakawa wasu da su kayi fashi da makami kwanaki a Garin Offa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 324

-Advertisement-

A Ranar Lahadi ne ‘Yan Sanda su ka sanar da cewa su na neman Bukola Saraki da ya bayyana a gaban su bayan wasu da ake zargi da yin fashi a wani banki a Jihar Kwara sun ambaci sunan sa a matsayin mai gidan su tun lokacin yana Gwamna.

Yanzu dai Shugaban Majalisar Dattawan ya bayyana cewa ya tashi har gaban ‘Yan Sandan ya wanke kan sa.

Tun da abin ya faru dai Sanatan yayi alkawarin bada hadin-kai.

A lokacin da ‘Yan Sanda suka ce suna neman Sanata Bukola Saraki yayi wuf yayi magana inda yace sharri Sufetan ‘Yan Sanda yake neman sa da shi domin babu yadda za ayi a matsayin sa na Shugaba ya hada kai ayi wa al’ummar sa ta’adi.

#Mikiya

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.