Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa kokarinsa na zurfafa dimokuradiyya ba a Najeriya kadai ba har ma da nahiyar Afirka, kamar yadda Yola24 ta rawaito.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Mallam Garba Shehu ya fitar.
Shugaba Biden ya bayyana haka ne a jiya Laraba a birnin Washington yayin ganawarsa da shugabannin kasashen Afirka shida da aka shirya gudanar da zabe a shekarar 2023 a gefen taron shugabannin Afirka da ke gudana a babban birnin kasar Amurka.
Add Comment