Labarai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari Ya isa Garin Daura Don Babbar Sallah

Buhari ya samu kyakkyawar tarba daga jama’an garin Daura

A ranar Laraba 30 ga watan Agusta ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa mahaifarsa a garin Daura don yin hutun babbar Sallah, inda ya hadu da dubun dubatan masoyansa da suke dakon isowarsa.

 

Sakamakon yawan jama’a da suka dabaibaye shi bayan saukarsa daga jirgi mai saukan angulu, shugaban kasa ya gagara shiga motarsa, wanda hakan ya sanya shi takawa tun daga wajen saukar jirgin zuwa gidansa.