Shugaban Hukumar EFCC Abdurrasheed Bawa, Ya Bukaci Ma’aikatan Bankunan Nijeriya Da Su Gaggauta Bayyana Kadarorinsu
Daga Comr Abba Sani Pantami
Hukumar EFCC ta umarci ma’aikatan banki da su bayyana kadarorinsu da suka mallaka ta kuma bada wa’adi zuwa ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2021, kamar yadda Jaridar The Cable ta ruwaito.
Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya ce sun tattauna kan kokarin da hukumar ke yi na kawar da laifukan kudi a kasar.
Bawa ya bayyana cewa an dauki matakin ne don duba rawar da bankuna ke takawa wajen rike kudaden da suka samu ba bisa ka’ida ba.