Labarai

Shugaban Ƙasar Turkiyya, Erdogan Ya Tura Sojoji 2000 Domin Yaƙar Isra’ila

Daga Tukur Sani Kwasara
Rahotanni daga Turkiyya na cewa, shugaba Reccep Erdogan ya bada umarnin kawar da Yahudawan Israila daga Ƙudus, baki ɗaya inda yace.

“Babu yadda za ayi kazo ka samu mutum a gidansa kuma ka nemi ƙwace gidan har ka riƙa yi masa kisan gilla don ka ga cewa duniya ta zuba maka ido, to mu ba zamu bari wannan zaluncin yaci gaba ba, saboda haka na baku umarnin nan da zuwa ƙarshen mako kuyi duk mai yuwuwa domin dawo da zaman lafiya a birnin Ƙudus da ma yanki baki ɗaya, idan ma ta kama ku kori duk wani bayahude daga birnin matuƙar ba zai baku haɗin kai domi a dawo da zaman lafiya a yankin ba” In ji shi kamar yadda ya bayyana a jawabin minti goma da ya yi a gaban shugabannin rundunar sojin ƙasar.

Wata kafar yaɗa labarai da ke da alaƙa da rundunar sojin ƙasar ta Turkiyya ta ruwaito cewa shugaba Erdogan ya bada umarnin tura kimanin sojojin ƙasar guda dubu biyu domin kawo zaman lafiya a yankin, inda kuma tuni suka kama hanyarsu ta zuwa yanki da asubahin yau, kafar ta ƙara da cewa “Akwai jiragen yaƙi guda 50 da tankokin yaƙi guda 400 da tuni sun isa yankin tun a daren jiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: