Labarai

Shugaban Ƙasar Nijer Ya Ba Da Umarnin Siyar Da Buhun Shinkafa ₦6,600

Rahotanni daga ƙasar Jamhuriyar Nijer Muhammad Bazoum, ya bada umarnin karya farashin buhun shinkafa a kasar inda ya ce daga yanzu buhun shinkafa ya koma kuɗin sefa jikka 7 da rabi wato 7,500FCEFA kimanin naira dubu 6,600 na Najeriya.

 Dama dai a makon da ya gabata ne gwamnatin ƙasar ta sanar da cewa ta bawa ƴan kasuwar ƙasar umarnin karya farashin kayan masarufi a faɗin ƙasar, sai kuma gashi yau an soma ganin umarnin a aikace.

Tuni dai al’ummar ƙasar suka fara shewa tare da murna kan wannan mataki da gwamnatin ƙasar ta ɗauka, sai dai a nasu ɓangare ƴan Najeriya, sun fara bayyana ra’ayinsu inda suke cewa wata miyar sai dai a maƙwabta.

Haarun

Haruna Lawan Usman is a certified Animal Health and Production Technologist, with more than 4 years experience in Animal Health and Production Technology.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: