-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Shugaba Buhari Yayi Magana Akan Bidiyon Ganduje


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A jiya Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana akan zargin da ake yiwa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje na karbar cin hanci daga yan kwangila, inda yace za’a dau mataki kan al’amarin.

Jaridar Daily Nigerian ta bada rahoton cewa Shugaba Buhari ya yi wannan magana ne yayinda wani dalibi dan asalin jihar Kano a kasar Faransa ya yabi irin ayyukan da gwamnan ya keyi musamman ta bangaren biya ma dalibai kudade suje waje suyo karati, inda har yayi kira akan gwamnati da ta kwaikwayi gwamnan wajen irin wadannan ayyukan.

Shugaba Buhari ya maida mashi da jawabi ta hanyar tambayar dalibin shin ya ga bidiyon da aka nuna gwamnan yana karban daloli?

Yace: “A bangare guda, shin baka ga bidiyoyin gwamnan inda yake cusa daloli cikin aljihun sa ba?”

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 653

- Advertisement -

“Mun baiwa hukumomin tsaro bidiyoyin domin bincike. Kuma za mu dau mataki akan abin indai aka same shi da kashi a gindi.”

Wannan furuci na shugaban kasa dai bai yiwa wasu dadi ba, ciki ko harda dan majalisan wakilan jihar Kano mai wakiltar Nasarawa, Nasir Ali Ahmed da kuma hadimin shugaban kasa Sha’aban Sharada, inda har suka bukaci yan jarida su taimaka su cire inda shugaba Buhari yayi wannan furuci.

Shin wannan furuci na shugaba Buhari na nufin cewa za’a hukunta Ganduje kenan?

#ArewaMobile

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: