-Advertisement-


Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Shugaba Buhari Yayi Kaurin Suna Wajen Take Hakkin Bil-Adama Da Cin Zarafin Dan Adam ~ Inji Kasar Amurka


0 605

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shugaba Buhari yayi kaurin suna wajen take hakkin Bil-Adama da cin zarafin dan Adam ~ Inji Kasar Amurka

Yayin da ya rage saura kwanaki kalilan shugaban kasar Amurka Donal Trump ya karbi bakucin shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari,

Gwamnatin kasar Amurkan ta fitar da wani rahoto dake nuna shugaba Buhari yayi kaurin suna wajen take hakkokin bil adama da cin zarafin dan Adam.

Premium Times ta ruwaito taken rahoton da
( ‘Rahotannin kasashe dangane da hakkokin dan Adam na shekarar 2017’,)
inda suka zargi gwamnatin Buhari da nuna halin ko in kula game da gudanar da binciken kwakwaf kan zarge zargen cin zarafin dan Adam, musamman wadanda ake zargin Sojojin Najeriya da tafkawa

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 324

- Advertisement -

“Gwamnati bata bincikar Yansanda, Sojoji da sauran hukumomin tsaro game da yadda suke amfani da karfi tare da makamai akan yan Najeriya, musamman masu gudanar da zanga zanga, duk kuwa da cewa gwamnatin ta kafa wani kwamiti don binciken take hakkin bil adama, amma har yanzu bata fitar da rahoto ba.”Inji rahoton

Sashin tsaro na gwamnatin kasar ta sanar da cewa gwamnatin Najeriya bata gudanar da binciken yadda aka kashe yan kungiyar fafutukar kafa kasar Biyafara, IPOB su 150, tare da kama daruruwan mutane, bugu da kari gwamnati ta yi biris da kisan yan shi’a da 348, da Sojoji suka kashe a Zaria.

Rahoton ya koka game da yadda ake neman yan kungiyar IPOB da yan shi’a ke yin batar dabo, aka neme su sama ko kasa, wanda rahoton ke zargin hukumomin tsaro da kame su, tare da kuma baiwa mutanen da suka kama horo mai tsanani

Rahoton da ya fito daga kasar Amurka ya bayyana damuwarsa da halayyar jami’an tsaron Najeriya, duk kuwa da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan wata dokar hana cin zarafin mai laifi a yayin gudanar da bincike.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.