Siyasa

SHUGABA BUHARI YAYI ALLAH WADARAI DA KALAMAN GWAMNA GANDUJE.

 

Daga Salisu Yahaya Hotoro

Shugaban kasa Muhammad Buhari yayi tur da Allah wadarai da kalaman gwamna Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje Wanda yayi a gidan gwamnatin jihar Kano wajen taron murnar dawowar Buhari gida Nigeria daga kasar Ingila.

Idandai zaku iya tunawa ranar alhamis data gabata ne 24/08/2017 mai taimakawa shugaba Buhari akan kafafen sadarwa Malam Shaaban Ibrahim Sharada ya shirya wani gangami domin nuna farin ciki tare da yin addu’o’i ga shugaba Buhari inda gwamna Ganduje yayi amfani da taron wajen furta kalaman zagi da cin zarafi ga tsohon mai gidansa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Gwamna Ganduje ya bayyana Kwankwaso a matsayin Wanda bayason shugaba Buhari ya samu lafiya kuma babban makiyi ga shugaban kasa Muhammad Buhari.

Inda a yammacin yau Shgaba Buhari ya kirawo Sanata Kwankwaso ta wayar tarho yake nisanta kansa da kalaman Gwamna Ganduje.

“Banji dadiba kuma banyi farin ciki da kalaman Ganduje ba, kuma ina mai tabbatar maka babu Wanda zai tsinka kyakkyawar alakar dake tsakanina dakai” cewar Muhammad Buhari.

Daga karshe Shugaba Buhari yayi godiya ga Sanata Kwankwaso da shawarwarin da yake bashi a gwamnatinsa, Sannan yayi hani ga yan siyasa dasu guji Labewa dashi suna cin mutuncin masu mutunci.