Labarai

Shugaba Buhari Ya Lashe Kyautar Gwarzon Gina Hanyoyi Na Shekarar 2021 A Fadin Afrika

Daga Ibrahim Da’u Mutuwa Dole
Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya lashe kyautar gwarzon gina hanyoyi na shekarar 2021, Shugaban zai amshi kyautar ne daga hannun takwaransa na ƙasar Egypt, Abdul-Fattah Al-Sisi wanda ya lashe shekarar data gabata.

Za’a miƙa kyautar ga wanda ya samu nasara a taron shekara-shekara na bankin AfDB ranar 24 ga watan Yuni, An bayyana shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe lambar yabon “Gwarzon mai gina hanyoyi 2021′ wacce akewa laƙabi da Trophée Babacar Ndiaye, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Shugaban ƙasar Najeriya ya ƙwace kyautar ne daga hannun shugaban ƙasar Egypt, Abdul Fatta Al-sisi wanda ya lashe kyautar a shekarar 2020.

A jawabin da bankin Africa AfDB ya fitar jiya, yace an bayyana sunan Buhari a matsayin wanda ya lashe kyautar a wajen buɗe taron masu gina hanyoyi ranar 31 ga watan Maris a Cairo, Egypt.

An ƙirƙiri wannan kyautar ne domin nuna girmmawa ga shugaban AfDB, Babacar Ndiaye, daga 1985 zuwa 1995.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: