Labarai

Shugaba Buhari Ya Jagoranci Zama Kan Harkar Tsaron Nijeriya

Daga Abubakar A Adam babankyauta
A yau Talata 30 ga watan Maris 2021 ne shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar tsaron Nijeriya a cikin fadar shi dake babban birnin tarayya Abuja.

Ana zaman ne a yayin da shugaba Buhari ke shirin tafiya birnin Landan, dake kasar Ingila domin duba lafiyarsa.

Daga cikin wadanda ke zaman akwai mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo; Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustpha; Ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi; shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; da mai bada shawara kan tsaron kasa, Babagana Monguno.

Haka zalika akwai shugaban hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor; shugaban Sojin kasa, Laftanan Janar Ibrahim Attahiru; shugaban Sojin ruwa, Vice-Admiral Awwal Zubairu; da shugaban mayakan sama, Air-Marshal Ishiaka Oladayo Amao.

Sauran sune Sifeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu; Dirakta Janar na hukumar DSS, Yusuf Bichi; Dirakta hukumar Leken asiri, Ambasada Ahmed Rufao Abubakar.

Muna rokon Allah ya tabbatar da alkairin dake cikin wannan tattaunawar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: