Wasanni

Shugaba Buhari Ya Cika Alkawarin Da Ya Dauka Na Raba Wa Tsoffin ‘Yan Kwallon Nijeriya (Super Eagles) Gidaje

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da ba wa tsoffin ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya (Super Eagles) da suka lashe gasar cin kofin Nahiyar Afrika ta 1994 kyautar gidaje masu dakuna uku-uku.

Shugaba Buhari ya ce ya cika alkawarin da ya yi wa ‘yan wasan ne saboda yadda suka jajirce a gasar da aka yi a Tunusia.

A cewarsa ”Wadannan ‘yan wasa sun fito da darajar Naieriya, kuma sun sa muna alfahari da ƙasarmu, don haka abun da za mu yi musu kawai shine cika alkawarin da muka yi musu”

Za a basu gidajen ne a duk inda suka zaba.

‘Yan kwallon na lokacin sune: Peter Rufai, Alloy Agu, Ike Shorounmu, Uche Okechukwu, Samson Siasia, Efan Ekoku, Sunday Oliseh, Benedict Iroha, Isaac Semitoje, Mutiu Adepoju, Emmanuel Amunike, Victor Ikpeba, Austin Eguavoen da marigayi Wilfred Agbonavbare.

Sauran sun hada da marigayi Uche Okafor, marigayi Thompson Oliha, marigayi Stephen Keshi, Christian Chukwu, Dr Akin Amao, Stephen Edema, Col. A Asielue da B. Aromasodun.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: