Labarai

Shugaba Buhari Ya Cancanci Yabo Musamman Ga Mu Mata Da Matasan Nijeriya, Cewar Hajia Ambaru Sani Wali Daura

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar Katsina da kasa baki daya, Hajia Ambaru Sani Wali Daura ta bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya cancanta a yaba masa musamman Mata da matasan kasar nan, saboda yadda kullum gwamnatinsa ke kokarin bunkasa rayuwar Mata da matasa a lungu da sakon kasar nan.

Hajia Ambaru Wali Daura ta bayyana haka ne a lokacin da take tattaunawa da manema labarai a gidan gwamnati jihar Katsina, jim kadan kafin a fara taron masu ruwa da tsakin na jam’iyyar APC ta jihar Katsina, kan shirin fara Yi wa membobin jam’iyyar rijista.

Hajia Ambaru, wadda ita ce ta fara yin kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito takarar a zaben 2015, ta ci gaba da cewa “hakika Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya cancanci yabo, ba kamar mu mata da matasa. Ni dai da wayauna, ban taba ganin mulkin da aka yi a kasar nan, aka rika tunawa da mata da matasa irin ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba, ta yadda aka kirkiro shirye-shirye daban-daban wanda za su amfana kai tsaye, duk ana cewa idan dambu ya yi yawa, bai jin mai, amma duk da hakan al’umma sun amfana, an bada tallafi da jari wanda bai kilguwa. Idan kai ko ke baki samu ba, makwabacin ka ya samu, kuma har zai iya zuwa wajenka. Muna godiya da irin wannan gagarumar guddumuwar da koyan sana’o’in hannu daban daban, duk an yi abin an yi shi akan faifai. Allah ya ba shi ikon sauke nauyi da ke wuyansa.

Babbar jigon ta APC ta kara da cewa Insha Allah ni a tunanin jam’iyyar mu ta APC za ta sake cin zaben ta a 2023, a kowane matakan saboda irin ayyukan alheran da jam’iyyar mu ta yi Kuma take cikin yi a halin yanzu, wanda Gwamnatocin baya suka kasa yi, kusan ayyukan sun karade lunguna da sakonta.

Hajia Ambaru Sani Wali Daura ta yi kira ga membobi jam’iyyar da ma masu sha’awar shiga jam’iyyar mu ta APC da su fito su yi katin jam’iyyar da ake shirin fara yi, saboda yana da matukar muhimmancin gaske. Kirana mai karfi ga Mata akan sabunta katin zama jam’iyyar, saboda duk abinda namiji ya yi mace na iya yinsa, takara tunda ta kansila har sama, sai dai wannan katin, saboda da zaran babu wannan katin ba ka cika cikkaken dan jam’iyyar APC ba.

Daga karshe ta yi addu’ar samun dawammamen zaman lafiya a jihar Katsina dama Nijeriya baki daya. Ta jawo hankalin yayan jam’iyyar APC su dunkule waje daya a samu hadin kai, saboda dukkan mu mun fito gida guda, mu guji san rai, saboda Yana kawo rabuwar kawuna, mu sani kuma Allah shi ke bada mulki ga wanda ya so a lokacin da ya so, mu hade kai waje daya mu zama tsintsiya madauri daya kamar yadda alamar jam’iyyar mu ta APC yake.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: