Sharhin Fina Finai

Shirin Furodusa Mukhtar Isa Na Samar Da Finafinai Biyu Lokaci Guda

advertisement

Daga Wakilinmu A daidai lokacin da ake ganin masana’antar finafinai  ta Kannywood ta karkata ga yin finafinai masu dogon zango, domin sayarwa ga manya gidajen talabijin da ake yayi a wannan lokacin sai ga shi furodusa Mukhtari Isah PRP mai kamfanin Bright Multimedia & Film Production yana gudanar da wani aikin finafinai har guda biyu wadanda suke masu gajeren zango ne. Kasancewar sa kwararren furodusa ne da ya dade ana damawa da shi a harkar, wannan ta sa ake ganin kamar furodusan ya ki tafiya da zamani ne domin kuwa a yada kida ya canja to  ya kamata a ce rawa ma ta canja, kuma zamani yakan zo da riga ne, wadda ake cewa idan ba ka saka ba, sia ka tafi tsirara.

To amma dai shi dai furodusa Muhtari Isah PRP da alama ya shirywa zaman shi ya sa yanayin aikin nasa ya yi daidai da irin kowane zamani, domin kuwa a yanzu ya yi nisa wajen aikin fim din Hadin Zumunci da kuma Lokaci Bako ne. don haka ne muka ji ta bakinsa game da irin shirin da ya yi a game da wannan aikin da ya sa a gaba, inda yake cewa;

“To, gaskiya na ade a wannan masana’antar kuma na yi aiki da yadda ba ma furodusin ba duk da cewar ba na furodusin din da nake yi aiki ne ake kawo min nake yi, amma a wannan lokacin na ga ya kamata na jarraba yin nawa, wanda yake kudi na ne na zuba nake gudanar a aikin a yanzu nake aikin kum ina sa ran nan da wata mai zuwa za a kammala kuma mun yi shirinn shigarsa kasuwa.

Ya ci gaba da cewa, “Kuma gaskiya maganar cewar na yi finafinai na kasuwa ba irin mai dogon zango da ake yi a yanzu ba, to akwai abu guda biyu da nake dubawa, na farko labarin finafinai masu inganci, marubucin labarin ya tsara labarin yadda sakon da yake cikin finafinan za su gamsar d masu kallo, sannan kuma an gina labari ne a kan matsalolin aure da ake fuskanta a yanzu, musamman ta fuskar zamantakewar iyali. Sannan kuma duk da cewar an koma fim na gidajen talabijin, hakan ba zai sa a aina yin fim na gida ba, don ko kasashe d ake ganin sun ci gaba ai ba su daina yin finafinai irin sa ba, to ka ga mu a nan ma ai yanzu aka fara, don haka wasu ba su da halin mallakar kayan kallon manyan gidan talabijin amma suna da DBD a suke yin kallo da shi don haka ba wai mun ki tafiya da zamani ba ne mu ne ma  muke tafiya da zamani, don in ka duba kayan aikin duk daya ne wajen inganci kuma an samu kwararrun ma’aikata.

Don haka abin da ake bukata kenan a cikin fim.” Nura Sharu shi ne Daraktan fim din Lokaci Bako ne, ya bayyana  mana cewar, “Gaskiya shi wannan fim da nake ba da umarni yana da sako mai muhimmanci, domin kuwa yana fadakarwa ne a kan matsala ta rashin fahimtarr juna a tsakanin miji da mata wadda idan abu ya samu maimakon a warware sai kowa ya dauki matakin ramuwa, wanda  hakan shi yake kara girman matsalar, har ta kai ga iyaye sun shiga cikin matsalar aboda sakin da yake shiga tsakani.

Wanda ba yadda shari’a ta tsara ba kenan.

Daga karshe ake  zuwa ga malamai suke warware matsalar ake fahimtar juna. Don haka nake ganin saokn fim din zai gamsar da masu kallo yadda ya kamata.” Ita ma jarumar fim din Lokaci Bako ne Maryam Isah Ceeter, ta bayyana mana  cewar, “Gaskiya na ji dadin wannan aikin musamman ma da na zamo ni ce jarumar fim din, saboda sakon da yake ciki ya zo daidai da matsalar da take faruwa a tsakanin ma’aurata na yi finafinai da dama, amma dai wanna sakon da yake cikin fim din Lokaci Bako ne ya fi dauke hankalina kuma ina fatan zai zama darasi ga ma’aurata a waje zamantakewar aure.”

Fim din dai ya kunshi jarumai da dama fitattun cikinsu akwai Bashir Nayaya Danmagori, Mustapha Musty, Maryam Isah Ceeter, Maryam Abubakar da sauransu.

#Hausaleadership

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button