Labarai

Shin PDP za ta iya kwace mulki daga APC a 2019?

Babbar jam’iyyar hamayya ta Najeriya, PDP, ta dauki hanyar magance rikicin shugabancin da ke cikinta bayan kotun kolin kasar ta ce Sanata Ahmad Makarfi ne sahihin shugabanta.

PDP ta fada rikici ne tun bayan da ta sha kaye a babban zaben kasar na 2015.

Amma yanzu hukuncin kotun kolin ya sa masu ruwa da tsaki a jam’iyyar na bugun kirji cewa za su kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC a shekarar 2019.

A wata hira da ya yi da BBC, Sanata Makarfi ya ce abin da za su sanya a gaba shi ne yadda za su hada kan ‘yan jam’iyyar da zummar karbar mulki daga hannun Shugaba Muhammadu Buhari.

“Wannan hukunci da kotun koli ta yanke ya ba mu kwarin gwiwar farfado da jam’iyyar PDP da zummar kwace mulki daga jam’iyyar APC, wacce da alama ba da gaske take son mulkar Najeriya ba”, in ji tsohon gwamnan na jihar Kaduna.

Sanata Makarfi ya kara da cewa PDP ita ce jam’iyyar da ta karade Najeriya don haka ba za su fuskanci matsaloli na sake tallata ta ba.

Da alama hakan ne ya sanya jam’iyyar ta PDP ta shirya wani taro a makon nan inda ta kafa kwamiti biyu kan yadda za a farfado da ita.

Wani jigo a jam’iyyar Sanata Abdul Ningi ya shaida wa BBC cewa sun gane kura-kuran da suka yi kuma a shirye suke su gyara su.

‘Mun yi nadama’

“Za mu sake yin taron koli na jam’iyya domin karawa shugabannin riko wa’adi domin su shirya yadda za a gudanar da babban taro. Ba ma so mu sake yin kura-kuran da za su sa wani ya kai mu kotu. Shi ya sa muka kafa kwamitin tsawatarwa saboda a baya ‘yan jam’iyyarmu ba su da da’a,” a cewar Ningi.

 

A cewarsa, daya kwamitin zai zagaya dukkan fadin Najeriya domin rarrashi da sasanta ‘yan jam’iyyar da aka batawa rai.

Sanata Ningi ya ce jam’iyyar ta yi nadamar jefa ‘yan Najeriya cikin wasu matsaloli, yana mai cewa duk da haka jam’iyyarsu ta fi APC yin mulki na gari.

Ya kara da cewa, “Mun yi damarar yin fito-na-fito da ko wacce jam’iyya. Za mu kwace mulki daga APC a 2019. ‘Yan Najeriya sun dandana kudarsu a hannun ‘yan jam’iyyar APC don haka ba za su sake yin kuskuren zabar jam’iyyar ba”.

Sai dai jam’iyyar APC ta ce da alama har yanzu PDP ba ta fahimci cewa ‘yan Najeriya sun gaji da ita ba kuma ba za su sake yin gangancin amincewa da ita ba.

Kakakin jam’iyyar Mallam Bolaji Abdullahi ya shaida min cewa, “hukuncin da kotun kolin ta yanke inda ta bai wa bangaren Sanata Ahmed Makarfi nasara shi ne ke yaudarar PDP take ganin za ta iya sake yin tasiri, amma ta manta cewa ‘yan Najeriya ba su manta da irin ukubar da ta jefa su a ciki ba”.

“PDP ce ta jefa kasar nan a cikin mawuyacin halin da take ciki: tabarbarewar tattalin arziki, rashin tsaro da rashin aiki da dukkan bala’in da muke ciki. A wurin su muka gaji dukkan matsaloli da muka tarar”, in ji Abdullahi.

Buhari da Tinubu ne sirrin karbuwar APC a arewa da kudancin Najeriya

Sai dai duk da wannan ikirari da Mallam Abdullahi ya yi na gadar matsaloli daga PDP, wasu ‘yan kasar na ganin jam’iyyarsa ta gaza daukar matakan magance matsalolin.

Hasalima wasu na ganin al’amura na ci gaba da tabarbarewa a hannun jam’iyyar ta APC.

Amma kakakin jam’iyyar ya ce, “Mun amince cewa ana shan wahala a kasar nan, amma ya kamata a sani cewa mun dauki matakan gyara matsalolin da muka tarar.

Lokacin da muka hau mulki jihohi da dama ba sa iya biyan albashi saboda faduwar farashin man fetur, amma mun yi kokarin magance wannan matsala, ciki har da na jihohin da PDP ke mulki”.

“Kazalika mun kusa magance matsalar rashin tsaro, musamman hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa.

“Ka duba irin kudin da aka kwato daga hannun tsofaffin jami’an gwamnatin PDP, wadanda suka sace kudin sayen makamai da kuma badakalar man fetur da ake zargin tsohuwar minista Diezani Allison-Madueke da hannu a ciki, inda ta wawure miliyoyin dala. Wannan shi ne irin mulkin PDP,” a cewar Bolaji Abdullahi.

A siyasance, kakakin jam’iyyar ta APC ya amince cewa jam’iyyarsu na fuskantar matsaloli, “amma mun kama hanyar magance su. Ba za mu taba yin rikici irin na PDP ba.

“PDP ce jam’iyyar da a wa’adin majalisa daya ta samar da shugabannin majalisar dattawa uku daban-daban saboda rikici. Haka kuma ita ce jam’iyyar da shugaban kasarta da mataimakinsa suka fada rikici”.

Abin da kamar wuya…

Masana harkokin siyasa dai na cewa dukkan jam’iyyun biyu na fuskantar kalubale a wurin ‘yan Najeriya.

Dr Sa’idu Ahmad Dukawa, Malami ne a Sashen koyar da kimiyyar siyasa na Jami’ar Bayero da ke Kano, kuma ya shaida min cewa: “Batun sake cin zaben PDP a kasar nan na da wuya domin kuwa har yanzu ‘yan Najeriya ba su manta da irin mawuyacin halin da da ta jefa su ba.

“Don haka idan APC ta dage wajen kawar da matsalolin tsaro tare da daure mutanen da ake zargi da sace kudaden kasar, lallai APC za ta ci gaba da mulki a 2019 ko da kuwa an ci gaba da fuskantar matsalolin tattalin arziki.

“Kar ka manta cewa ko a lokacin soja, ‘yan Najeriya suna kaunar Shugaba Buhari ne saboda ya daure azzalumai”.

Amma masanin siyarar ya ce idan APC ta kuskura ta bari mutanen da ake zargi da sata suka sha, za ta fuskanci gagarumin kalubale wajen sake karbuwa a wajen ‘yan kasar.

“Haka kuma ‘yan kasar, wadanda suka dana mulkin jam’iyyun biyu, za su yi la’akari da wacce jam’iyya ce ta fi faranta musu rai kafin su sake zabe.

Wani abu kuma shi ne yadda PDP ta koyawa APC al’adar cewa idan kana kan mulki ba ka faduwa zabe.

“Idan ka duba zabukan kananan hukumomin da aka yi kwanan baya za ka ga cewa babu inda APC ta fadi. Don haka ya rage ga PDP ta samo hanyar kawar da wannan al’ada,” in ji Dr Dukawa.

Abin jira a gani dai shi ne hukuncin da ‘yan Najeriya za su yanke domin kuwa wuka da nama suna hannunsu.