Labarai

Shin Nigeria za ta iya sayen makamai daga Amurka?

Donald Trump ya ce shugaba Najeriya ya cancanci yabo dangane da yaki da ta’addanci.
A ranar Litinin ne dai shugaban Amurka, Donald Trump ya yi wata tattaunawa da takwaransa, Muhammadu Buhari na Najeriya kan batutuwa da dama da suka hada da yadda za a kulla sabuwar yarjejeniya kan makamai domin taimaka wa Najeriya ta yaki da ta’addanci.
Da sabuwar gwamnatin Amurka, Najeriya na da damar ta kara kaimi wajen yakin da take yi da kungiyar ‘yan Boko Haram.
Yakin da sojojin Najeriya ke yi da kungiyar Boko Haram ya samu nakasu sakamakon wasu takunkumi da Amurkar ta saka wa kasar a baya.
Amurka ta aike wa Najeriya da masu bai wa sojoji shawara da horarwa kan sanin makamar aiki.
Amma dokar majalisar Amurka da ke hana kasashen da ake zargi da keta hakkin bil adama, ta Leahy, ta hana Amurka sayar wa Najeriya makamai.
Ana zargin sojojin Najeriya da keta ‘yancin dan adam, duk da dai cewa ba kudin goro aka yi wa duka makaman wajen haramta sayar da su ba.
Dokar ta kuma hana wasu kasashenta sayar wa Najeriya makamai, kafin a sauya a karshe.
A wani bangaren kuma, Amurka ta hana Isira’ila sayar wa Najeriya jiragen Amurka masu saukar ungulu na yaki.
Najeriya ta dora alhaki kan Amurka na rashin nasarar da ta yi a yakinta da Boko Haram kuma hakan ya tursasa mata neman taimako daga kasashen da suka hada da Ukraine da Rasha da Belarus.
Najeriya ta yi hakan ne domin kasashen su taimaka mata da makamai da bai wa sojojinta horo.
Domin kulla sabuwar yarjejeniya da Najeriya, Amurka tana da zabi na ko ta kaucewa yin amfani da dokar Leahy ko kuma ta kara duba tarihin da sojojin kasar ke da shi a kan take ‘yancin dan adam domin ta dawo da sayar mata da makaman.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement