Kimiyya

SHIN KUNSAN ‘YAN 419 SUN FI YAWA A HARKAR KASUWANCIN YANAR GIZO?

Daga Abdulrahman Muhammad Sharada 

A kwanan nan na ga da yawan mutane sun mayar da hankalin su akan hanyoyin samun kudi ta yanar gizo, abin ya zama kamar wutar daji, da yawan mutane kuma ba su san abin ba kawai daga an ce ana samun kudi sai su tura kansu, wasu ba sa bincike kawai shiga suke, duk da akwai wadanda addini ya yarda da su wasu kuma kawai karya ce da damfara tsagwaronta.

TARIHI A TAKAICE

Michael Aldrich ya mutu a shekarar 2014 shine mutum na farko da ya kirkiri online shopping a shekara 1979, daga baya kuma mutane irin su Brain Action, Larry Page, Sergey Brin, Even Spiegel’s da sauransu suka kirkiri abubuwa da za ka shiga domin zuba hannun jari ko kuma ka yi kasuwanci a yanar gizo, siya ko siyarwa.

A yanzu babu wanda zai iya fada maka adadin manhajar da ake irin wannan sabgar a duniya suna da tarin yawa, kamar su chipper cash, Spin &win zeraklamy, Big Time cash, swag bucks, upwork, thredup, cardpool, gazelle, swap, offerup, your work, forex, bitcoin, coins, moth cash da sauransu

KALA KALAR SU

Akwai na zahiri akwai kuma wadanda ake kirkira domin damfara, akwai wadanda idan ka shiga kamar kanka kayiwa tsirara, wasu kuma idan ka shiga kamar ka tonawa asusunka asiri ne,akwai wadanda idan ka bude tamkar ka gayyato wa hanyoyin sadarwarka yan harkars ne, kai akwai wadanda shi kansa wanda ya kirkira bama a san shi ba, kuma yayi haka ne domin tara abin duniya, kuma ya cuci mutane

Akwai cigaba insha Allah zan warware abubuwan da yadda ya  kamata idan kanaso kayi zaka bi, saboda kada ka tura kanka halaka, ko kuma ka kai kanka ga hanyoyin cin haramun a matsayinka na musulmi.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement