– Shugaban kungiyar daliban Najeriya (NANS), Chinonso Obasi ya bayyana cewa a hira da yayi da fadar shugaban kasa kwanan nan, Buhari zai dawo kan aikinsa nan ba da jimawa ba
– Shugaban kungiyar na NANS ya shawarci ‘yan Najeriya da su bi abunda ya dace a fafutukarsu kan lafiyar shugaban kasa
– A cewar Obasi, ya kamata a dauki rashin lafiyar Muhammadu Buhari a matsayin abun da zai zo ya wuce a kasar
Chinonso Obasi, shugaban kungiyar daliban Najeriya ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a, a maimakon yi masa fatan mutuwa, NTA ta ruwaito.
Arewablog.com ta tattaro cewa a wata sanarwa wanda aka saki a Abuja, Obasi ya bayyana cewa bisa ga hira da yayi da fadar shugaban kasa a ranar 22 ga watan Yuli, Buhari zai dawo kwanan nan, kamar yadda yake samun lafiya sosai.
A cewar Obasi, bai kamata ba yadda aka mayar da lafiyar Buhari siyasa.
Obasi yaroki ya kamata a dauki rashin lafiyar Muhammadu Buhari a matsayin abun da zai zo ya wuce a kasar.
Add Comment