Labarai

Shin Kama Shekau Shine Karshen Boko Haram?

Shin Kama Shekau Shine Karshen Boko Haram?

Daga Maje El-Hajeej Hotoro

Ina fatan alheri ga shugaban sojoji na Nijeriya Laftanal Janar Yusuf Tukur Burutai dangane da himma gami da kwazo na yaki da Boko Haram.

Jim kadan bayan furta kawo maka Shekau a raye ko a mace ya sa ‘yan Najeriya da dama bayyana ra’ayin su akan wannan batu.

Daga masu cewa, ba mamaki kun gano inda ya ke, sai masu fadin ya na hannun ku kawai so kuke wa’adin ya cika ku fito da shi.

Sai masu yakinin ba za ma ku iya kama shi ba, kawai hira ce. Wasu kuma cewa suke yi, wannan sakon karfafa gwiwa ne ga rundunar sojojin a matsayin kara jajircewa fiye da wacce suke yi.

1. Ko ma me za a fada Burutai ya zama shugaban sojoji mafi tasiri a wajen ‘yan Najeriya. Wanda ya samu shaidar girmamawa daga sassan duniya sakamakon bajintar sa na yaki da Boko Haram. Shin Burutai zai iya kawo karshen Boko Haram? Shin sojoji za su iya cika wa’adin da ya ba su na kawo Shekau a raye ko a mace? Wannan duk lokaci ne zai tabbatar da hakan.

 

2. A wata tattaunawa da na taba yi da Farfesa Dahiru Yahaya na sashin koyar da tarihi a jami’ar Bayero da ke jihar Kano, ya bayyana cewa, Boko Haram duk duniya ake yi ba a Najeriya kadai ba. Kana kuma bugu da kari, bindiga ba za ta kawo karshen wannan akida ba. Domin mutum ya fi bindiga karfi.

Ga duk mai bibiyar al’amuran yau da kullum na duniya, baya bukatar karin bayani na yadda kungiyoyi masu irin akidar Boko Haram suka mamaye duniya.

3. A Wa’azin Sheikh Ja’afar Mahmud Adam (na Suratul Tauba) ya kawo misalin wani mai tsananin zafin akida da ya ke ganin Imanin sa ya kai ya ci gyaran Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam yayin da ya ke rabon ganima. ‘Ka yi adalci’ shine sakon sa ga Annabi.

Yayin da Sayyidina Umar (Allah Ya yarda da shi) ya fusata gami da fuskantar sa, sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, ya dakatar da shi. ‘Masu irin wannan akidar suna nan ko uwar su ma ba a haifa ba’ (ma’ana za su zo nan gaba)

4. A wata lakcar Sheikh Abdurrazaq Yahaya Haifan ya yi bayanin cewa, masu irin wannan akida za su wanzu har tsawon lokacin tashin Alkiyama, illa iyaka Allah Ya daukarwa kansa alkawari cewa, duk yadda suka kai da karfi zai karya su, sai dai wani lokaci gaba suka kara farfadowa.

5. A lakcar Dr. Sani Rijiyar Lemo da ya taba gabatarwa a birnin Maiduguri dangane da kungiyoyin masu fafutukar kafa Jihadi, ya zayyano salsalar yadda suke wanzuwa daga wannan mataki zuwa wancan da kuma yadda akidar ta yadu a duniya.

6. Ba marigayi Muhammad Yusif ne ya kawo akidar Boko Haram Najeriya ba, ya gaje ta ne kamar yadda Shekau ya gaje ta. Akida ce da aka aka dauko ta gami da rainon ta tare da busa ta ga mutane. Wacce kuma ko an kashe Shekau ko an kama shi za ta ci gaba da yaduwa, saboda akwai masu ita a wasu sassan duniya kullum suna aikin busa mata numfashi. Kamar yadda ba bangaren Shekau ne kadai Boko Haram a Najeriya ba.

7. Su waye iyayen tafiyar? A ina suke? Me ya sa suke yi? Me suke son cimma? Ta ya suke shigo musu da tallafin kudi da makamai? Ta ya suke samun bayanan tsaro na sirri? Su waye mabiyan su? Ta ya suke jan ra’ayin su? Asiri? Kudi ko akida?

8. Shin ba ma mamakin yadda a bidiyon su muke ganin matashi ya na cike da murna da farin ciki sakamakon zaben sa a matsayin wanda zai mutu ta hanyar kai kunar bakin wake? Ba ma mamakin yadda ragowar matasan ke cike da bakin ciki yayin da su ba a zabe su ba? Ba ma mamakin yadda ake zuwa daya bayan daya ana rungumar wanda aka zaba a matsayin gwarzo kuma jarumi? ‘Ku bar ni na tafi domin ina jiyo kamshin Aljanna’ ba ma mamakin yadda cike da zumudi ya ke gaggawar tafiya domin ya kashe wasu shima ya mutu?

9. Shin muna mamakin a jerin bidiyon su muke ganin matasa masu karancin shekaru suke sarrafa manyan kayan yaki na zamani? Ina suka samu? Ta ya aka shigo musu da su? Wa ye ya ba su? A ina kuma aka ba su horo? Shin ba ma mamakin irin kwarin gwiwar da suke da shi na tunkarar yin gumurzu da gwarazan sojojin mu? Me ya ba su wannan kwarin gwiwar?

10. Shin ba ma matukar mamakin yadda a bidiyon su ake nuna yadda suka zabi rayuwa cikin duhuwar daji babu wata doka sai dokokin da suka yi daidai da akidar su?

11. Shin ko mun taba tunanin cewa, Boko Haram fa tamkar gwamnati suke, akwai tsarin jagoranci daga shugaba, mataimaki, Kwamandoji, sashin shari’a, sashin zartaswa, sashin yada labarai, sashin leken asiri, sashin dakaru, sashin daukar sabbin mabiya, sashin horas da mabiya, sashin wa’azi, sashin harkokin kudi da makamai, sashin kasuwanci da sauran su.

12. 12. Shin yin sulhu da su ne mafita? A sakar musu kwamandojin su a ba su kudi? Gobe ma su kama wasu su ce sai an ba su kudi an sakar musu mutane? Ko kuwa a ci gaba da yaki ne suna kashewa ana kashe su? Ko kuwa za a kashe Maciji ne a kuma sare kansa?

13. Ga masu zagin sojojin Najeriya akan sun gaza bai yi musu adalci ba, ga mai jiran yau ko gobe a gama da Boko Haram ya sake tunani, ga mai fatan alheri kada ya yanke kauna, ga mai muradin amfani da ayyukan su domin sha’anin siyasa ya tabbata wawa kuma mahaukaci.

14. Idan har sauran kasashen duniya daban-daban da suka fi Najeriya karfin tattalin arziki da izzar mulki ba su tsira ba ina ga mu? Idan har za su kashe sojojin Amurka da Ingila da sauran kasashe da suka fi sojojin Najeriya samun horo da kayan yaki ina ga namu?

15. Mayakan Boko Haram suna da dabaru da hikimomi na zamani, sun iya sarrafa na’urori na yaki da na sadarwa. Suna yawo a yanar gizo tare ganin bayanai kamar yadda sauran mutane ke yi. A wani mataki ma sun fi sauran mutane ilimin amfani da yanar gizo da na’urar Zamani.

16. Laftanal Janar Yusuf Tukur Burutai shugaban rundunar sojojin Najeriya ne ba shugaban rundunar sojojin Aljanu ba da zai yi fiye da abinda yanzu ya ke yi.

Allah Ya tsare mana Imanin mu Ya kuma tsare mana kasar mu baki daya.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement