-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Shin Dama Can `Yan Kwankwasiyya Masoya Buhari Ne Ko Angulu Kan Zabo Suka Yi?


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kungiyar siyasar Kwankwasiyya dake cikin jam’iyyar PDP zata iya zuwa ta biyu a Najeriya wajan tara jama’a masu yawa idan aka zo yakin neman zabe, watau bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari wanda shine na daya.

Kungiyar ta yi karfi sosai a jihar Kano inda har ta tsallaka wasu jihohi makwauta. Shugaban ta, tsohon gwamnan jihar Kano, a duk sanda zai yi taron siyasa akan ga dubban mutane sanye da jar hula sun yi taro na ban mamaki.

Koda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da ya je yakin neman zabe jihar ta Kano an ga taro na ban mamaki.

Saidai sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Kano, ya saka alamar tambaya akan biyayyar da ‘yan Kwankwasiyyar ke wa jagoran nasu ko kuma ace uwar jam’iyya, watau PDP.

Lura da yawan kuri’un da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya samu a jihar Kano, cibiyar Kwankwasiyya, za’a iya cewa ‘yan kwankwasiyyar kodai dama can masoya shugaban kasa Muhammadu Buharine ko kuwa sun yi Angulu da kan zabo.

Dama dai jihar Kano ta kasance jihar da a tarihi ta fi baiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari yawan kuri’u, to amma a wannan karon, ganin cewa Kwankwaso baya tare da Buharin a jam’iyyar APC, an yi tsammanin yawan kuri’un zai canja.

Idan dai da gaske jama’ar da ake gani a taron yakin neman zaben Kwankwasiyya ‘yan kwankwasiyyar ne to akwai dayan cikin abubuwan-

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 25

- Advertisement -

Kodai dama basu da katin zabe.

Ko kuma Buhari suka zaba.

Ko kuma sunki fitowa su yi zabe.

Hakan ya kara tabbatuwa ne bayan duk yan takarkarun da Kwankwaso ya tsayar suka fadi zabe cikin harda dan takarar sanatan da Kwankwason ya tsayar wato Aliyu Sani M/Gini don maye kujerar da yake kai shima ya fadi zaben.

Dama dai tuni wasu ke ganin cewa Tsohon gwamnan Kanon, Kwankwaso ya tafka kuskure barin jam’iyyar APC da yayi, saboda kallo na biyu da ake mai bayan Buhari. Kuma ana ganin hakan zai iya mai illa a siyasance ta yadda zai rasa mabiya da yawa.

 

Abin jira a gani sh

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: