Labarai

Shin Baba Buhari Ya Samu Labarin Mutuwar Janar Attahiru?

Daga Haji Shehu
Tun bayan Jana’izar babban hafsan Sojan kasan Najeriya tare da sauran abokan aikin sa yau a birnin tarayya Abuja, sai na fara tambayar kaina cewar ‘Baba Buhari ya samu labarin Mutuwar waɗannan Zaratan masu hidimtawa kasa kuwa?

Na yiw kaina wannan tambaya ce duba ga yadda na zura na mujiya ina dakon ganin sa a wajen Jana’izar waɗannan mutane masu tarun albarka da Muhimmanci ga kasa.

Bayan gane cewar Baba Buhari bai halarci wannan jana’iza ba, sai na fara tambayar kaina da cewar, kilan Baba Buhari bai samu labarin mutuwar su ba, domin idan har ya samu watakila zai halarci Jana’izar duba ga hidimar da suka yiwa kasa.

Ganin cewa a watan Janairun 2016, Baba Buhari ya halarci bikin tunawa da sojojin Kenya 100 da Alshabab suka kashe, sai na kyautata masa zaton cewar idan har ya samu labarin Rasuwar Attahiru, babu abunda zai hana shi zuwa Jana’izar Attahiru.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: