Jarumar hausa film Halima Atete Ta zama Queen Of Kannywood yayinda Jarumi Ali nuhu yake King Of kannywood.
Jaruma Halima Atete ta zama sarauniyar kannywood, ya yin da Ali Nuhu shine sarki. anyi wannan nadin sarautar agarin Bauchi da kuma Kano.
Wanda taron nadin ya tara manyan jarumai maza da mata, anyiwa jarumar nadin ne domin jajircewarta da kwazonta da take nunawa acikin masana’antar hausa fim, anyi nadin akarkashin jagorancin shugaban matasan kannywood Alasan Kwalli, da kuma inuwar matasan kannywood.
An gudanar da zaben ne bisa saka kuri’a da masu jagorantar kungiyar kannywood suka yi, sun la’akari da abubuwa masu tarin yawa kafin su zabi Halima Atete amatsayin sarauniyar kannywood, babban abinda aka duba shine gudumawar da ta bayar tun lokacin da ta shigo masana’antar hausa fim.
Amma wasu masu harsashe akan abinda ya shafi harkokin hausa fim da daba’i sunce anyi kuskure wajen nada Halima Atete, domin akwai jaruman da sukafi ta bayar da gudumawa acikin kannywood. koma dai maye yanzu Halima ce ”SARAUNIYAR KANNYWOOD”.
Add Comment