Shekararsa 40 Yana Yi Wa Kungiyar Kwallon Kafa Ta Kano Pillars Hidima

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Daga Ahmad M. Deedat

Wannan shine Baba Bala wanda aka fi sani da Sarkin Ruwa Abala’u. Mutum ne wanda ya dade yana bada gudummawarsa a wajen nuna kaunarsa da tsananin bautawa club din Kano Pillars.

Talla

A tattaunawarmu da shi, ya bayyana cewa tun shekarar 1977 yake tare da Works FC dake filin Gandun Sarki a cikin sakatariyar Audu Bako. Shi yake zuwa ya sanya musu raga a kullum ta Allah. Haka har zuwa yau ya cigaba da hidimtawa kungiyar Kano Pillars wacce ta maye gurbin Works FC da Raca Rovers Kano.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 54

Sai dai abin mamakin mahunkunta masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa a Kano musamman na kungiyar Kano Pillars ba su nuna kulawa da irin tsantsar soyayya da hidima da ya yi wa kungiyar ba tsawon shekaru 40.

Ya kamata a duba wannan bawan Allan a kuma yaba masa bisa kokarinsa da jajircewarsa.

CC:
Alh Tukur Babban gida
Alh Ibrahim Galadima
Lurwanu Malikawa Garu
Musa Bestseller

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: