Sheikh Gumi Ya Yi Wa El-Rufai Raddi Kan ’Yan Bindiga

0 0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Suleiman Abba (TBABA)

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi raddi ga Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da sauran masu sukar shawararsa ta yin sulhu da ’yan bindiga.

Da yake jawabi kan shawarwarin da ya bayar kan hanyoyin kawo karshen ta’addancin ’yan bindiga, malamin ya ce bai taba yin kira cewa gwamnati ta biya ’yan ta’adda diyya ba.

Sheikh Gumi ya bayyana cewa ’yan bindiga sun hada da barayi, ’yan fashi da kuma masu ta da kayar baya, wadanda ya ce su ne kashi 90% na ’yan bindiga Fulani.

Idan ba a manta ba, a ranar Litinin Gwamna El-Rufai ya soki shawarar malamin na yin sulhu da ’yan bindiga da Fulani a yankin Arewa maso Yamma da malamin kuma abokinsa ya bayar.

El-Rufai, a hirarsa da Sashen Hausa na BBC, ya ce Fulanin ba su san addini ba kuma babu wanda ya tsokane su, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi sulhu ko biyan su diyya ba sai dai ma ta yake su.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 782

Sheikh Gumi, ya ce yawancin makiyaya sun koma daukar makamai ne saboda shekarun da aka dauka jami’an tsaro na zaluntar su, suna kashe su da dabbobinsu, kona gidajensu da cin kudadensu.

Fitaccen malamin ya kara da cewa an samu gagarumar nasar a tattaunawar da ya yi da makiyaya a ziyarar da ya kai musu a cikin dazukan Jihar Zamfara.

Ya ce makiyayan sun ba shi tabbacin ajiye makamansu matukar gwamnatin jihar za ta samar musu da cikakken tsaro.

“Mutane ne da ke fama da tashin tashin hankali, don haka suka dauki makamai don kare kansu.

“Duk inda suke a matsayinsu na makiyaya suna fuskantar matsala da manoma; mun ga abin da ya faru a Oyo, inda aka kona gidajensu da shanunsu.

“Suna zaune ne a cikin bukkoki wadanda ke kashe su da rusa gidajensu kuma na zaune a gidaje na alfarma,” inji shi.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: