Labarai

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Yaba Wa Gwamna Mai Mala Kan Inganta Makarantun Tsangaya A Jihar Yobe

Daga Haruna Sardauna

Kwamitin tuntuna da neman hadin kan Malamai da Sarakunan Gargajiya, kan tsarin sirka karatun boko da Addini, karkashin jagoranci Kwamishinan Ma’aikatar Ilimin Makarantu Firamare da Sekandire, Dr. Sani Idris, ya Isar da Saqon Sheikh Dahiru Usman Bauchi ga Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yabawa Gwamnan jihar Yobe Hon. Mai Mala Buni bisa kokarin da Gwamnatin shi take na farfadowa da inganta tsarin ilimin tsangaya na karantar da Alku’ani da Hadisan Manzon Allah.

Shehin Malamin ya yi jinjina a Gwamnan ne, a lokacin da tawagar Kwamitin tuntubar neman shawara suka sauka a fadar Malamin dan neman shawarwari da tabarraki.

A lokacin ziyarar tawagar Kwamitin zuwa fadar Shehin Malamin, Shehin yayi musu Tuni bisa alkairi da Gwamna Buni yayi lokacin da aka fara korar Almajirai daga Wasu Jihohin arewa kan Cutar Corona-Virus, ya yabawa Gwamna Bisa kirar da yayi a Kawo mar dukkan Almajiran da aka kora a jihar sa, Ya kar6i Almajiran Kuma yayi musu hidima, kuma ga tsarin daya dauko na Inganta Makarantu tsangaya.

A sakon da Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya aiko a Gwamma Buni, kamar yadda Kwamishina Dr. Sani Idris ya fada, Shehin Yace Gwamna Buni “Zaiga Sakayyar Yin Hidima A Alku’ani Mai Tsarki”, wannan saqon ya kara karfin guiwa a gwamnan bisa manufofin sa na Inganta Karatun Tsangaya, ta hanyar samar da abubuwan Bukata a Malamai da Almajiran makarantun tsangaya na fadin jihar Yobe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: