Wato Jama’a a jiya Lahadi 17 ga watan Janairu 2021 Sheikh Data Ahmad Mahmud Gumi ya je dajin Kangimi domin yada da’awa ga Fulani mazauna kauyuka akan Karantarwar addinin musulunci.
Kamar yadda muka sani ne ita da’awa hanya ce wacce Annabi Muhammad S.A.W ya yi amfani da ita domin yada addinin musulunci a fadin duniya baki daya. Sannan hanya ce mai matukar hadari ga mutumin da ya dauke ta a matsayin aikin sa a nan duniya. Domin sai ya gamu da adawar makiya musulunci ta fuska daban-daban.
Don haka muna rokon Allah ya baiwa rayuwar Sheikh Dakta Ahmad Gumi kariya daga makircin makiya musulunci.
Daga Abubakar A Adam Babankyauta