Sheikh Abdujabbar Ya Maka Ganduje A Kotu Bisa Rufe Masa Masallaci

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Suleiman Abba (TBABA)

Sheikh Abdujabbar Nasiru Kabara ya maka Gwamnatin Jihar a gaban a Kotu, saboda hana shi wa’azi da kuma rufe majalisinsa da ke masallacinsa a Jihar.

Abduljabbar na neman kotun ta tabbatar masa na hakkinsa tare da hana gwamnatin da kuma ’yan sanda ci gaba da rufe masallacin nasa da kuma hana shi yin wa’azi.

Bayan sauraron karar a ranar Laraba, Kotun wadda Mai Shari’a Lewis Allagoa ke jagoranta ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar Alhamis 18 ga Fabrairu, 2021.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 693

Kotun ta kuma ba da umarnin mika sammaci ga Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano da kuma Kwamishinan ’Yan Sanda, wadanda su ne malamin ya shigar kara.

A makon jiya ne Gwamnatin Kano ta ba da uamarnin hana malamin yin wa’azi nan take saboda zargin sa da cin zarafin Sahabban Manzon Allah da kuma neman tayar da fitina a Jihar.

Ta kuma hana shi yin irin wadannan karatuttuka, ta hana kafafen yada labarai sawa a Jihar sannan ta rufe masallacinsa inda majalisinsa na As-habul Kahfi yake.

Abduljabbar na kalubalanta matakin ne da cewa tauye masa hakkin da doka ta ba shi ne na bayyana ra’ayi, walwala da gudanar da tarukan lumana.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: