Shehu Sani Yayi Allah Wadai Da Kin Sa hannun Buhari Yayi A Sabon Kudirin Tsarin Zabe

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Sanata Shehu Sani wanda ke wakiltar Yankin Jihar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawan kasar nan ya tofa albarkacin bakin sa game da kudirin sauya dokar tsarin zabe da Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma yin watsi da shi.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
Talla

Hukumar Karota Ta Kama Mota Cike Da Tabar Wiwi

1 of 661

Sanatan na Jam’iyyar PRP yayi tir da matakin da Shugaban kasar ya dauka na kin sa hannu akansabon kudirin tsarin zaben da Majalisar Tarayya ta aiko masa.

Shugaban kasa Buhari yayi watsi da kudirin ne a Ranar Juma’ar nan data gabata .

Shehu Sani ya bayyana cewa cin amanar tsarin Damukaradiyya ne a ce Buhari yayi fatali da wannan kudiri da zai gyara harkar zaben kasar.

Sanatan ya ba Shugaban kasar shawara da ya guji biyewa wadanda ke kokarin murde zaben 2019.

Sanatan yayi wannan jawabi ne a shafin sa na sadarwa na Tuwita bayan Shugaba Buhari ya maidawa Majalisa kudirin zaben a wannan karo.

Kwamared Shehu Sani yace akwai masu gudun ayi zaben ke-ke-da-ke-ke a Gwamnatin APC.

‘Dan Majalisar yayi mamakin yadda Gwamnatin nan ke gudun ayi zaben adalci a badi, ganin cewa irin wannan zabe na kwarai ne ya jawo APC tayi nasara.

Sanatan ya kuma koka da yadda ake muzgunuwa ‘Yan adawa a halin yanzu.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: